Friday, 8 December 2017

Nigeria: An yankewa wasu mutane biyu masu yima yara fyade daurin rai dai rai a Bauchi


Wata babbar kotu a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin
Najeriya ta yankewa wasu mutum biyu hukuncin daurin rai da
rai a gidan yari bayan samun su da laifin aikata fyade.

Kotun ta samu mutunen ne da laifin yi wa wata mace mai
shekara 40 fyade tare da kwakule mata ido.
Lamarin dai ya faru ne a garin Dass a shekarar 2014.
An shafe shekara biyu ana tafka shari'ar inda alkalin kotun ta
bayyana mutanen biyu a matsayin marasa imani da ya ce bai
kamata suna cudanya da al'umma ba.
Jama'a da dama dai sun yi marhabin da hukuncin da suka ce
zai zama darasi ga wasu da ke aikata fyade.
Matsalar aikata fyade dai matsala ce da ta zama ruwa dare a
Najeriya, sai dai ba kasafai ake hukunta wadanda suka aikata
laifin ba.
Kungiyoyin fararen hula sun sha gudanar da zanga-zanga kan
yadda al'umma a Najeriyar ke yin wasa-rai-rai da karuwar fyade a kasar.


Uploaded by abdulazeez alkasim Umar:

Sunday, 3 December 2017

News updates:Atiku Abubakar ya koma PDP


Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar
ya koma jam'iyyar adawa ta PDP.

Dan siyasar ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Facebook
ranar Lahadi.
Sai dai bai fito fili ya bayyana anniyarsa ta sake neman
shugabancin kasar a babban zaben kasar na shekarar 2019.
Ya ce ya koma jam'iyyar ne saboda matsalolin da suka sa ya
fice daga PDP a shekarar 2014 "an warware su yanzu."
Har ila yau ya ce jam'iyyar APC ta "kasa cika alkawurran da ta
yi wa al'ummar kasar musamman matasa."
 baya dai Atiku Abubakar ya sha sauya jam'iyyun siyasa.
Kuma wannan ne karo na biyu da dan siyasar yake koma wa
jam'iyyar PDP.
Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban Najeriya ne
tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.
A shekarar 2007 ne ya fara tsakayawa takarar shugabancin
Najeriya ne a karkashin jam'iyyar AC.
Hakazalika ya sake neman takarar a shekarar 2011, amma bai
samu tikitin jam'iyyarsa ta PDP ba.
Atiku Abubakar ya kara neman tsayawa a shekarar 2014, inda a
nan ma bai samu tikitin shugabanci ba a karkashin jam'iyyar
APC.




Domin samun sauran labarai kadanna Rubutunnan mai kala


Domin samun labarai gameda harkar ilimi kadannaRubutunnan mai kala