Friday, 10 November 2017
'Yadda aka tsaga gabana aka sa magani domin mallakar miji'
Wata matar aure wadda ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida
wa Fatima Zahra Umar a shirin Adikon Zamani cewa, "ba ta
taba samun ikon mallakar mijinta ba sai lokacin da ta je wurin
wata mai maganin mata na gyaran gida ta tsaga mata
gabanta tare da sanya magani a ciki."
Ta ce "duk matan da suke cewa kayan mata ko kuma gyaran
jiki karya ne to ba su san dawan garin ba ne kawai."
Irin wannan batu na gyaran jiki ko kuma tsare gida da mata ke
yi na janyo kace-nace a tsakanin magidanta har ma da
malaman addini.
Cikakkiyar hirar za ta zo muku ne a shirinmu na Adikon Zamani
a ranakun Asabar da Lahadi da karfe 7:30 na safe agogon
Najeriya da Niger.
Da fatan za ku kasance da mu domin jin cikakkiyar hira da
wannan mata da sauran mata da ma kuma ita mai yin tsagun.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment