Wednesday, 8 November 2017
Nigeria: Zanga-zangar 'yan tasi ta tsayar da al'amura a Abuja
Wata zanga-zanga da direbobin tasi suka yi ta tsayar da
al'amura a Abuja, babban birnin Najeriya, inda aka kona tayoyi
tare da hada cunkoson motoci a sassan birnin da dama.
Tarzomar ta samo asali ne bayan da direbobin suka zargi
jami'an rundunar hadin gwiwa ta birnin da kisan daya daga
cikinsu.
Kawo yanzu dai jami'an rundunar ba su ce komai ba kan
wannan zargi. Kuma yunkurin BBC na ji daga bakin jami'an ya
ci tura.
Wannan batu ne ya kai ga rufe babbar hanyar da ta hada
sassan birnin da babbar kasuwar Wuse, abin da ya sa birnin ya
cunkushe.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan birnin ya shaida
wa BBC cewa za su fitar da sanarwa nan gaba kan lamarin.
Shi kuwa wani dan kusuwa da ke harkokinsa a kasuwar ta
Wuse ya shai da wa BBC cewa sun shiga fargaba saboda
tsoron kada wani abu ya shafi dukiyarsu.
Ya kara da cewa 'yan kasuwa da dama ba za su yi ciniki kamar
yadda suka saba ba, saboda tsaikon da aka samu.
Babu tabbas kan mataki na gaba da masu zanga-zangar za su
dauka nan gaba.
A yanzu rahotanni sun nuna cewa al'amura sun fara lafawa.
An dade ana samun sabani tsakanin jami'an wannan runduna
da kuma masu motocin haya, inda masu motocin ke zarginsu
da ci musu zarafi.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment