Monday, 6 November 2017

Kamfanoni 800,000 ba sa biyan haraji a Nigeria - Kemi Adeosun

                 
A yayin da Najeriya ke bin matakan rage dogaro da arzikin
fetir, gwamnatin kasar ta ce ta gano kamfanoni kimanin
800,000 da ba su taba biyan haraji ba, wadanda da suka hada
da na 'yan Kwangila.

Wata takarda da ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun ta
rubuta, kuma aka raba wa manema labarai kan hanyoyin
bunkasa tattalin arzikin Najeriya, ta ce yanzu haka gwamnati
na binciken kwakwaf a kan kamfanonin.
Sai dai kuma ba a bayyana sunayen kamfanonin ba, ko kuma
irin ayyukan da suke yi.
Wani jami'in hukumar karbar haraji ta kasa ya shaidawa BBC
cewa babban kalubalen da suke fuskanta shi ne gano adireshin
kamfanonin duk da cewa suna da rijista.
Ya ce a reshen ofishin hukumar da yake kula da shi kawai a
Ikoyi a Lagos, akwai kamfanoni sama da 8000 da aka gano
cewa ba su taba biyan haraji ba.
Ko da yake Jami'in ya ce Lauyoyi ne ke taimaka wa
kamfanonin kaucewa biyan haraji domin suna masu rijista ba
tare da sun tantance adireshin da kamfanonin suke ba, da
kuma manufar kafa kamfanin, lamarin da ke bai wa jami'an
hukumar karbar harajin wahala.

No comments:

Post a Comment