Saturday, 11 November 2017

Wanda ya fallasa dalolin da EFCC ta gano a Lagos ya 'zama miloniya' IKON ALLAH!!!.


Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin
Najeriya ta'annati ta ce mutumin da ya fallasa kudin da aka
gano a wani gida a unguwar Ikoyi da ke jihar Legas "ya zama
miloniya."
Shugaban riko na hukumar, Ibrahim Magu, ne ya tabbatar da
haka a wani taro a birnin Vienna na kasar Australiya, in ji
sanarwar da mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren,
ya fitar.
Uwujaren ya tabbatar wa BBC cewa hukumar ta bai wa wanda
ya fallasa boye wadansu makudan kudade a wannan gida,
amman ya ki ya bayyana nawa aka bai wa mutumin.
A shekarar da ta wuce ministar kudin Najeriya, Kemi Adeosun,
ta bayyana shirin gwamnatin kasar na bayar da tukuicin kashi
biyar cikin 100 ga duk wanda ya fallasa "haramtaccen kudin"
da ake zargin na sata ne.
Idan aka yi la'akari da cewa kudin da aka samu a gidan na
Legas a farkon shekarar nan ya kai naira biliyan 13, za a iya
cewa wanda ya kwaramata bayanin kudaden zai samu kimanin
naira miliyan 650 (kashi 5 cikin 100 na kudin da aka samu a
cikin wani bene a Legas).
Bayan hukumar EFCC ta yi wawan kamun ne dai aka gano
cewa kudaden suna da alaka da tsohon shugaban hukumar
leken asirin Najeriya ta NIA, Ayo Oke.
Wannan ya sa shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sa
aka dakatar da Mista Oke daga farko, kuma ya kore shi daga
baya.

No comments:

Post a Comment