Sunday, 12 November 2017

Labari da dumiduminsa-An gano diamond da nauyinsa ya kai karat 400 a Saliyo


Masu hakar ma'adinai a Saliyo sun hako wani diamond wanda
nauyinsa ya kai karat 476, kuma an ce shi ne diamond na 29
ma fi ya girma da aka gano.
Kawo yanzu dai kwararu basu tabbatar da darajar ko kuma
kudin diamond din ba.
Lamarin dai na zuwa ne bayan da aka gano wani daimaond da
nauyinsa ya fi karat 700, wanda shi ne diamon mafi girma da
aka gano a Saliyo a cikin rabin karni.
A watan gobe dai zaa ayi gwajonsa a birnin Newyork na
Amurka.
Shugaban hukumar ma'adinai ta kasar Saliyo, Sahar Wonday ya
ce diamond din da aka gano ya nuna cewa akwai albarkatun
kasa masu daraja a yankin Kono, inda a nan ne aka gano
dukannin daimond din su biyu.
Kasar na son tayi amfani da cinikin watan Disemba domin ta yi
kokarin kawar da abubuwan da suka faru a baya watau yakin
basasa da aka shafe shekara 11 ana yi wanda kasuwanci
diamond na cikin abubuwan da suka rika ruruta rikicin.

No comments:

Post a Comment