Wednesday, 8 November 2017

Mota ta afka aji, yara biyu sun mutu

                                       
                             

  • Wasu yara biyu maza 'yan shekara takwas sun mutu bayan da

mota ta afka cikin wani aji a wata makarantar firamare a
Sydney.
'Yan sandan kasar sun ce hadarin wanda da ya faru ne a
makarantar gwamnati ta layin Bankisa ya raunata yara mata
uku wadanda yanzu su na asibiti.
Hukumomi sun ce likitoci masu bada agajin gaggawa sun
duba sauran yara 19 da ke ajin a take a wajen.
Matar da ke tuka motar wata mata ce 'yar shekara 52, kuma an
kai ta caji ofis. Hukumomi a garin sun ce ba sa tunanin cewa
hadarin ya faru ne da gangan.
Hadarin ya faru ne misalin 09:45 a ranar Talata (22:45) agogon
GMT ranar Litinin a yankin Greenacre.
Likitoci masu bada agajin gaggawa sun bayyana inda hadarin
ya faru a matsayin "waje mai tsananin rikicewa".
Wasu yara biyu maza 'yan shekara takwas sun mutu bayan da
mota ta afka cikin wani aji a wata makarantar firamare a
Sydney, in ji 'yan sanda.
Hadarin da ya faru a makarantar gwamnati ta layin Bankisa ya
raunata yara mata uku wanda yanzu su na asibiti.
Hukumomi sun ce likitoci masu bada agajin gaggawa sun
duba sauran yara 19 da ke ajin a take a wajen.
Wata mace 'yar shekara 52 ce take tuka motar, kuma an kai ta
ofishin 'yan sanda. Hukumomi a garin sun ce ba sa tunanin
hadarin ganganci ne.
Likitoci masu bada agajin gaggawa sun bayyana inda hadarin
ya faru a matsayin "waje mai tsananin hadari".
"Bisa dukkan alama, waje ne na tsananin tashin hankali" a
cewar wata ma'aikaciyar hukumar bayar da agaji na gaggawa
na New South Wales (NSW) Ambulance Sufirtanda Stephanie
Radnidge.
"An samu wasu yara da malamai da su ka shiga matsanancin
tashin hankali da damuwa a wurin da hadarin ya faru".
Samun kula
An kai yaran maza biyu asibiti, inda a nan ne su ka rasu
sakamakon raunukan da su ka samu. Wata yarinya 'yar shekara
tara na cikin matsanancin hali, yayin da wadancan biyun 'yan
shekara takwas sun samu sauki.
'Yan sanda sun ce kadan daga cikin yaran sun samu kananan
raunuka kuma an kula da su a take a wajen da hadarin ya faru.
Abun na da tsananin wahala saboda mu kanmu iyaye ne, kuma
mu mutane ne" in ji Sufirtanda Radnidge.
"Amma mu na da matukar horaswa kuma mun bayar da
kulawa ta musamman ga wadnda su ka samu raunuka da
safen nan."
'Yan sanda sun ce za a yi wa matukiyar motar gwaje-gwajen
jini da na fitsari, kuma su na binciken yadda hadarin ya faru.
"Ba mu yarda cewar wannan hadarin da gangan ya faru ba" inji
Shugaban 'Yan sanda na New South Wales, Kwamanda Stuart
Smith.
Har yanzu dai hukumomi ba su kai ga tantance ko matar na da
wata alaka da makarantar ba.
Wani mutum da ya ke wajen a lokacin da abun ya faru, Khaled
Arnaout, ya ce, ya ga wani babban rami a jikin bangon ajin
bayan da yai ta jin ihu na fitowa daga wajen.

No comments:

Post a Comment