Magidancin ya kashe mahaifiyar sa mai shekari 100 tare da
taimakon mahaifin shi bisa ga zargin kashe diyar shi ta hanyar
tsubbu
Hukumar yan sanda a jihar nija ta kama wani magidanci Likita
Manu mai shekaru 40 wanda ya kashe mahaifiyar sa kan
zargin kashe mai diyar ta hanyar tsubbu.
Jaridar punch ta kawo rahoto cewa an kama Manu tare da
mahaifn sa Kwacha mai shekaru 80 wanda ya taimaka masa
wajen dukan mahaifiyar har numfashin ta ya dauke.
Labari ya nuna cewa manu ya hau mahaifiyar shi da duka bisa
ga zargin kashe mai diya ta hanyar tsubbu.
Shima mahaifin sa Kwacha ya taimaka mai wajen aikata laifin
wanda yayi sanadiyar mutuwar matarsa. An kama su ne bayan
karar da makwabta suka kai ga rundanar yan sanda.
yayin da yake bada amsar tambayoyi a ofishin yan sanda
mahaifin ya shaida cewa yarinyarb itace mutum na tara da
matarsa Kaiyo ta kashe ta hanyar tsubbu kuma ba wai yayi
niyan kashe ta ba, lamarin ya faru ne bayan ya nemi ya dan
zane ta da icce bisa ga abun da tayi da jikan sa wanda ya
fusatar dashi.
Da aka tambeyi shi ta yaya ya gano cewa mahaifiyar shi ta
kashe diyar shi Manu yace:
"Mun gano ta hanyar diyata Magajiya yayin da take jinyar wata
rashin lafiya. Tana ta kuka tare da rokon kakar ta Inne Kaiyo da
ta saki ruhin ta.
Muma mun roke ta amma taki amincewa. kuma ina sane cewa
mahaifiya ta mayya ce."
Jami'in hulda da jama'a na rundunar Asp Abigail Adaeze ta
tabbatar da lamarin kuma tace za'a gurfanar dasu gaban kotu
bayan an gama bincike akan su.
CLICK HERE TO GET MORE NEWS
No comments:
Post a Comment