Wednesday, 8 November 2017

Iran na takalarmu da yaki - Saudiyya

   
                               

Yariman Saudiyya Mohammed Bin Salman ya zargi Iran da
talakar yaki ta hanyar samar da makamai masu linzami ga
'yan tawayen Yemen.
Yariman ya danganta matakin a matsayin yaki, kamar yadda
kafofin yada labaran Saudiya suka ambato shi yana shaidawa
sakataren harakokin wajen Birtaniya Boris Johnson ta wayar
tarho.
A ranar Asabar an kakkabo wasu makamai masu linzami kusa
da Saudiyya.
A nata bangaren, Iran ta musanta zargin bai wa 'yan tawayen
Houthi makamai wadanda ke fada da gwamnatin Yemen da ke
samun goyon bayan dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta.
Ministan harakokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya
danganta kalaman Yariman a matsayin ma su hatsari.
Wasu kafofin yada labarai da ke goyon bayan 'yan tawayen
Houthi sun ruwaito cewa mayakan sun harba Burkan H2, wani
nau'in makami mai linzami a filin saukar jirgi na Sarki Khaled
da ke arewa maso gabashin Riyadh, wanda ke nisan kilomita
850 daga kan iyaka da Yemen.
Sai dai Saudiyya ta yi nasarar kakkabo makamin, yayin da
wasu tarkacensa suka warwatsu a filin saukar jirgin.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta ce harba makamin mai
linzami a tashar jirgin saman da fararen hula suke, ya kasance
aikata laifukan yaki.
Yarima Mohammed wanda ya yi Allah-wadai da harba
makamin, ya ce yunkurin gwamnatin Iran na samar da manyan
makamai ga 'yan tawayen Yemen tamkar mataki ne na
kaddamar da yaki akan masarautar Saudiyya.
Minsitan harakokin wajen Iran Javad Zarif, ya yi tir da kalaman
na Yarima a zantawar da ya yi da Mista Johnson ta wayar
tarho bayan ministan harakokin wajen na Birtaniya ya tattauna
da Yarima a ranar Talata.
Iran da Saudiyya sun dade suna yakin cacar-baka musamman
kan karfin ikon mulki a Gabas Ta Tsakiya.
Kuma duk da cewa kasashen ba su taba yaki da juna ba amma
a fakaice suna yakar juna ta hanyar goyon bayan bangarorin da
ke rikici a wasu kasashe.

No comments:

Post a Comment