Saturday, 11 November 2017

Ba za mu manta da gwamnatin Buhari ba —inji yan Shi'a


Wani mabiyin mazhabar Shi'a a Najeriya da aka fi sani da
Islamic Movement of Nigeria, IMN karkashin jagorancin
Sheikh Ibrahim Elzakzaky, ya ce ba za su taba mantawa da
'rashin adalcin' da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya
yi musu ba dangane da al'amarin da ya faru tsakaninsu da
sojoji a Zariya.
Ahmad Bawa Jalam ya ce da shi da sauran mabiya jagoran
IMN ba za su gushe ba face suna addu'ar neman sakayya daga
Ubangiji.
A ranar 10 ga watan Disambar 2015 ne dai sojojin suka yi
zargin almajiran Sheikh Zakzaky da tsare wa babban hafsan
sojin kasar, Janar Yusuf Tukur Buratai hanya da kuma kokarin
hallaka shi.
Bayan nan ne kuma sojojin suka far wa gidan shugaban na
IMN, sheikh Elzakzaky bisa dalilan bayanan sirri da suka samu
da ke nuna mabiya mazhabar ta Shi'a na shirin daukar matakin
kai hare-hare, al'amarin da ya janyo kisan mabiya mazhabar da
dama sannan kuma aka kama shugaban kungiyar da har yanzu
ke tsare a hannun gwamnati.
Sojojin dai sun ce mutum takwas ne suka mutu sakamakon
samamen, a inda bakwai daga ciki 'yan Shi'a ne sannan kuma
guda daya soja.
Sai dai kungiyar IMN ta musanta alkaluman a inda da farko ta
ce an kashe mata 'ya'ya fiye da 500 sannan kuma daga bisani
ta ce an kashe kusan mutum dubu daya.
To amma wani kwamitin bin bahasin hakikanin abin da ya faru
da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa ya gano abubuwa da dama
da suka hada da kisa da binne mabiya mazhabar ta Shi'a 347 a
asirce.
Wannan ne ya sa mabiya jagoran na IMN, kamar Ahmad Bawa
Jalam ke ganin shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ba zai
taba kubuta daga zarginsu ba.
Ku saurari hirar na yi da Ahmad Jalam:
Matsayin kotu kan Elzakzaky
A watan Disamban 2016, wata babbar kotu a Abuja ta nemi
gwamnati ta saki Elzakzaky da matarsa tare da biyan sa diyya
sannan kuma a gina masa gida, a duk garin da yake so a
arewacin kasar, duk a cikin kwanaki 45.
To amma har yanzu gwamnati na ci gaba da tsare Elzakzakyn
bisa wasu dalilai da ministan Shari'ar kasar, Abubakar Malami,
ya ce ta dogara da su.
"Idan irin wannan ya faru a kan rinjayar da bukatar al'umma
fiye da ta mutum guda," in ji Malami.
Ya kara da cewa "Idan an bayar da oda ko kuma hukunci, ya
zama an daukaka kara akwai bukata wadda doka ta amince da
ita na ainihin wanda bai gamsu ba ya nemi dakatar da zartar
da hukunci."
Ga dai yadda hirar tasa ta kasance da Editanmu na Abuja,
Naziru Mika'ilu:
Da man dai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo
ya ce ba za su saki jagoran IMN ba duk da kotu ta ce a sake
shi, bisa dalilan shari'a da na tsaro
Me lauyoyi ke cewa?
Masana shari'a da dama dai na ganin ya kamata gwamnati ta
yi adalci sannan kuma ta girmama kundin tsarin mulki sannan
su kuma mabiya Shi'a su yi hakuri su bi doka tunda dai
gwamnati ta ce za ta kalubalanci hukuncin kotu.
Barista Sunusi Musa, wani lauya mai zaman kansa a Najeriya
ya ce, "Tunda dai gwamnati ta ce za ta daukaka kara sannan
kuma ta gindaya batun tsaro, lallai ya kamata mabiya Shi'a su
kwantar da hankalinsu su ci gaba da neman hakkinsu ta hanyar
tsarin dokar kasa."
Sai dai kuma Barista Sunusi ya kara da cewa, "Ni a ra'ayina zan
so a ce an saki Elzakzaky domin bin umarnin kotu."
"Wani lokacin akwai bukatar gyara a harkar shari'ar Najeriya
saboda bai kamata a ce kotu ta bayar da umarni ba amma a ki
bin sa," in ji Sunusi Musa.
Matsayin  kungiyoyin 'yancin danadamg
Kungiyoyi masu fafutukar kare 'yancin dan adam a Najeriya da
ketare kamar Amnesty International sun fito balo-balo suna
zargin gwamnatin Najeriya da rashin mutunta 'yancin mabiya
Shi'a.
Da man dai kungiyar Amnesty International ce ta fara fadin
cewa ta gano wurin da aka binne 'yan Shi'ar da aka kashe a
Zariya, a asirce.
A har ko yaushe kuma kungiyar tana ci gaba da sukar ci gaba
da tsare shugaban IMN, Ibrahim Elzakzaky ba tare da gurfanar
da shi a gaban kuliya ba domin ya fuskanci hukunci.
A baya-bayan nan ne kuma aka kara samun wasu kungiyoyin
masu rajin kare hakkin dan adam da ke cikin Najeriya kamar
Concerned Citezens suka yi ta gudanar da zanga-zanga iri-iri
tare da mabiya Shi'a domin neman a saki Elzakzaky.
Zanga-zangar neman sakin Elzakzaky
Tun dai kama da tsare jagoransu a watan Disambar 2015,
mabiya mazhabar Shi'a suke ta fama gudanar da taruka da
zanga-zanga iri-iri domin a bi musu kadinsu da kuma sakin
shugabansu da ma sauran 'yan kungiyar da suka yi zargin suna
tsare.
Ma fi yawancin lokuta dai 'yan Shi'ar na haduwa da fushin
jami'an tsaro a inda suke tarwatsa su bisa dalilin cewa 'yan
Shi'ar ba sa neman izinin hukuma.
Sannan kuma suna shiga hakkin mutane ta hanyar tsare
hanyoyi ga matafiya.
To amma Barista Sunusi Musa ya ce, "Duk da cewa ko wane
dan Najeriya yana da hakkin gudanar da taro ko nuna
damuwarsa ga wani abu idan dai har ba zai karya doka ba ko
kuma ya take hakkin wani, ya kamata 'yan Shi'a su rinka sanar
da jami'an tsaro kafin gudanar da zanga-zanga domin jami'an
tsaron su ba su kariya."
Sai dai mai magana da yawun IMN, Ibrahim Musa ya ce, "Babu
inda aka ce sai ka shaida wa jami'an tsaro za ka gudanar da
taro ko zanga-zanga."
Ya kuma ce, "Batun a ce muna tare hanya wannan kuma ba
haka ba ne kawai dai makiyanmu ne suke fada domin samun
abin da za su soke mu da shi."
A baya dai shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi kira
ga jami'an tsaron kasar da su yi taka-tsan-tsan wajen dakile
ayyukan 'yan Shi'a.
Gwamnatin jihar Kaduna da IMN
Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa wani kwamitin bin bahasin
hakikanin abun da ya faru tsakanin sojoji da 'yan Shi'a a Zariya
kasancewar garin na karkashin jihar.
Kwamitin kuma ya gano abubuwa da dama da suka hada da
kisa da binne mabiya mazhabar Shi'a 347 a wasu wawaka-
wawakan ramuka na bai daya.
Sannan kuma ya bayar da shawarwari masu yawa kan yadda
za a guji afkuwar irin rikicin a gaba.
Shawarwarin dai sun hada da hukunta jami'an tsaron da suka
aiwatar da kisan 'yan Shi'a a Zariyar da haramta kungiyar 'yan
uwa musulmi ta IMN tare kuma da hukunta shugabanta,
Elzakzaky.
Tuni kuma gwamnatin jihar ta haramta gudanar da ayyukan
kungiyar sannan ta sha alwashin hukunta Elzakzaky, kamar
yadda a baya-bayan nan gwamna Nasir Elrufa'I ya shaida wa
wata kafar talbijin a Najeriyar cewa, "Muna jira gwamnatin
tarayya ta miko mana Elzakzaky domin mu samu mu gurfanar
da shi a gaban kotu."
To sai dai har kawo yanzu gwamnatin ba ta aiwatar da
shawarar hukunta sojojin da suka kashe 'yan Shi'ar ba kamar
yadda kwamitin ya bukata.
Hakan ne ya sa lauyan Elzakzaky, Femi Falana ya nemi da
gwamnatin ta jihar Kaduna da hukunta jami'an tsaron.
A wata sanarwa da ya aike wa da BBC, Mista Falana ya ce,
"Dole ne a hukunta jami'an tsaron da suke da hannu a kisan
Zariya, idan kuma ba haka ba to za su gurfanar da su a gaban
kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC."
Ya ya za a warware rikicin Shi'a da gwamnati?
Masana a fannin shari'a kamar Barista Sunusi Musa na ganin
za a iya shawo kan rikicin gwamnati da 'yan Shi'a ta hanya
biyu:
Sulhu
Shari'a
Dangane da sulhu, Barista Sunusi Musa ya ce, "Gwamnati za ta
iya zama da Elzakzaky da mabiyansa a tattauna, kamar yadda
aka yi da tsagerun Naija Delta. Idan abin ya kama a bayar da
diyya sai gwamnati ta bayar tun da mun ga yadda aka yi kan
kisan sirikin shugaban Boko Haram, Muhammadu Yusuf, a inda
gwamnatin jihar Borno ta bayar da diyyar naira miliyan dari."
To amma Sunusi ya kara da cewa, "Ita ma gwamnati za ta iya
zayyana wa jagoran Shi'ar irin bukatunta sannan dole ne
Elzakzaky da mutanensa su martaba dokar kasa."
Abin kuma da ya shafi shari'a, Barista Sunusi ya ce, "Idan har
sulhun bai yiwu ba sai a je ga matakin gurfanarwa a gaban
kotu, idan kotu ta same shi da laifi ta hukunta shi, idan kuma
ba shi da laifi ta sake shi."
Illar rikicin Shi'a da gwamnati ga tsaron kasa
Masana harkar tsaro a Najeriya sun ce idan dai har ba a bi
matakan da masana shari'a suka zayyana ba wajen warware
takaddamar Shi'a da gwamnati, to fa kasar za ta fada cikin
wani hali.
Dr. Kabiru Adamu, wani masanin tsaro ne a Najeriya kuma ya
zayyana matsalolin da Najeriya za ta iya fadawa idan har rikicin
Shi'a da gwamnati ya ci gaba da wakana:
"Idan Elzakzaky ya mutu a hannun gwamnati, babu
makawa 'yan Shi'a za su ce gwamnati ce ta kashe shi
saboda haka Allah kadai ya san abun da zai faru."
"Rashin magance wannan rikici zai iya janyo mummunan
rikicin banbancin akida tsakanin Shi'a da Sunna kamar
yadda ake gani a wasu kasashen gabas ta tsakiya."
"Al'amarin zai iya sanya wasu kungiyoyin addini su fara
shirin kare kai, kafin gwamnati ta zo kansu su ma."
Abin da 'yan Shi'a ke bukata
Mai magana da yawun Islamic Movement of Nigeria, Ibrahim
Musa ya shaida wa BBC cewa, "Muna da bukatu da yawa
amma dai babbar bukatarmu yanzu haka ita ce a saki
jagoranmu, Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa da sauran 'yan
uwan da ake tsare da su", a inda ya ci gaba da fadin, "alabashi
idan aka sake shi to sauran bukatun shi ya san yadda za a yi
da su."
Sharhi
Masana a fannin shari'a da tsaro dai sun daki jaki da kuma
taiki kan rikici tsakanin 'yan shi'a da gwamnati.
Yayin da Dr Kabiru Adamu ya ke ganin, "Najeriya ta yi amfani
da karfi fiye da kima wajen dakile ayyukan tsirarun mabiya
Shi'a", shi kuwa Barista Sunusi Musa ya ce, "Dole ne 'yan Shi'a
su san cewa bin doka dole ne a matsayinsu na 'yan Najeriya."
Sai dai kuma Barista Sunusi ya kara da cewa, "Gwamnatin
Najeriya ita ma ya kamata ta san cewa 'yan Shi'a suna da
'yancin yin addinin da suka ga dama."
A yanzu dai a iya cewa, al'ummar kasar ta zura ido ne don
ganin ya ya za ta kaya tsakanin gwamnati da kungiyar IMN kan
batun sakin jagoran nasu da sauran 'yan uwansu da aka kama,
musamman a daidai wannan lokaci da Shugaba BUhari ya cika
shekara biyu a kan mulkin kasar.

No comments:

Post a Comment