Saturday, 11 November 2017

yanzu soja ne ke mulkin Nigeria –wole Soyinka


Farfesa Wole Soyinka ya ce Shugaban Najeriya Muhammad
Buhari har yanzu bai zama "cikakken farar hula ba, ta
halayyarsa ga sauran al'ummar kasar gabadaya."
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da Jimeh Saleh ,
Editan sashen Hausa na BBC, yayin da ya kawo mana ziyara
ofishinmu na Landan, kwanakin baya.
Ya ce shugaban ya gaza wajen shawo kan matsalar kiraye-
kirayen raba kasar da kungiyar IPOB ke yi.
Farfesan ya ce har yanzu kasar tana amfani ne da kudin tsarin
mulki wanda ya samu asali daga sojoji. "Kudin tsarin mulki ne
da sojoji suka yi wa kansu," a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa: "Har yanzu sojoji suna rike da manyan
mukamai a kasar ciki har da kujerar shugaban kasa."
"Fata muke su mayar da kansu fararen hula ciki da bai. Kuma
wannan yana daya daga cikin gazawar Shugaba Buhari," in ji
shi.
Shugaba Buhari ya taba zama shugaban mulkin sojin Najeriya
a tsakanin shekarar 1983 zuwa 1985, kafin ya lashe zabe a
shekarar 2015.
Har ila yau, farfesan ya ce shi bai ga dalilin da ya sa za a ci
gaba da tsare jagoran 'yan Shia Sheikh Ibrahim Zakzaky ba,
kuma "hakan kuskure ne."
Kimanin shekara biyu ke nan da gwamnatin kasar take tsare da
malamin bayan rikicin mambobin kungiyarsa da sojojin kasar a
Zariya.
Sai dai ya ce duk da cewa akwai fannoni da dama da
gwamnatin Buhari "ta tafka kurakurai wadanda suka cancanci
suka, akwai kuma fannonin da ya kamata a yaba mata".
Ya ba da misali da yadda gwamnati ta yi aiki wajen gano kudin
da aka sace wadanda aka kai kasashen ketare.
Da kuma yadda aka sa "wadansu manyan jami'an gwamnati
suka amayar da kudin da suka sace".
Hakazalika farfesan ya ce shugaban zai iya cewa ya cika aikin
da aka zabe wato aikin yaki da cin hanci da rashawa da kuma
shawon kan rikicin Boko Haram da kuma makamantanta.

No comments:

Post a Comment