wani magidanci ya shiga hannun --hukuma bayan yayi lalata da
diyar sa bisa ga umarnin bokaye
An gurfanar da wani magidanci Bashiru Adeyanju a gaban
kotun majistere dake Ado-ekiti a jihar Ekiti bayan ya amince
cewa yayi lalata da diyar shi mai shekaru 17 bisa ga umarnin
bokaye domin ya samu arziki.
Bisa ga rahoton Tribune , Adeyanju ya amsa laifi cewa yayi
lalata da diyar kusan so 9 kana bokayen suma sunyi farna da
ita duk cikin tsarin neman kudi ta hanyar tsubbu.
Adeyanju wanda yace neman arziki yasa yayi lalata da diyar sa
kuma bai ji dadi ba ganin cewa shi kadai aka gurfanar gaban
ko yayin da bokayen suka tsere.
“Mu uku muka aikata laifi, amma nayi mamaki da na gana ni
kadai yan sanda suka gurfanar a gaban kotu” inji adeyanju.
Shugaban kotun Mrs Dolapo Akosile ta tabbatyar mai cewa
za’a gabatar da saura abokan aikin shi.
“Kada ka damu, za’a kawo saura gaban kotu”.
A bisa ga labarin Adeyanju, akwai wata farar kyallen hankicif
da yake shafar farjin diyar duk lokacin da ya sadu da ita kamar
yanda bokayen suka umarce shi, duk da cewa ya aikata haka
lokaci da dama shidai wannan magidancin bai cinma burinsa
na samun arziki.
Jami’in dan sanda da ta gurfanar da shi Sergeant Monica
Ikebuilo tace wanda ake tuhuma ya aikata laifi da ya sabawa
kundin tsarin mulkin jihar kuma ta roki kotu da a daga karar
har zuwa lokacin da hukumar dake yanke hukunci ta bada
shawara akan laifin.
Shugaban kotu ya bada umarni na a cigaba da rikon mai laifin
a gidan yari har zuwa ranar 12 ga watan Octoba bayan anji
shawarar hukumar zata bada.
Domin samun labarai kadanna WANNAN Bulan rubutu.
No comments:
Post a Comment