Tuesday, 14 November 2017
Ba zan yi watsi da al'ummar Igbo ba - Buhari, inji shugaban kasa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai yi watsi
da al'ummar Igbo da ke kudu maso gabashin kasar a duk
tsawon mulkinsa.
Da ya ke magana a lokacin da ziyarar da ya kai yankin,
shugaban ya ce zai cika dukkan alkawuran da ya daukar wa
jama'ar yankin.
"Kamar yadda na fada a baya... Ina sake jaddada wa cewa ba
zan yi watsi da ku ba". Ya kara da cewa "Najeriya kasarmu ce
mu duka".
Al'ummar yankin dai sun sha zargin gwamnatin shugaban da
nuna musu banbanci, lamarin da jami'ai suka sha musanta wa.
Wannan ce ziyara ta farko da Shugaba Buhari ya kai yankin tun
bayan hawansa mulki. Kuma ta zo ne duk da barazanar da
kungiyar fafutikar kafa kasar Biafra ta IPOB ta yi masa na tayar
da tarzoma a lokacin ziyarar.
An dai tsaurara matakan tsaro a jihohin Ebonyi da Enugu da ya
ziyarta, kuma kawo yanzu babu wani labarin tashin hankali.
A ranar Laraba ne ake sa ran shugaban zai ziyarci jihar
Anambra inda zai halarci taron yakin neman zabe na dan
takarar gwamna na jam'iyyarsa ta APC.
Wasu dai na cewa Shugaba Buhari ya ziyarci yankin ne domin
halartar taron yakin neman zaben, amma makusantansa sun
musanta.
Ra'ayoyin jamar yankin dai sun sha bambam kan wannan
ziyara, inda wasu ke maraba da ita, yayin da wasu kuma cewa
shugaban ya yi latti.
Akasarin mutanen da BBC ta zanta da su ta wayar tarho sun ce
suna wa Shugaba Muhammadu Buhari maraba a wannan ziyara
ta farko da zai kai yankin.
Wasu Igbo dai sun sha sukar Muhammadu Buhari kan yadda
suka ce ba ya damawa da al'ummar yankin a gwamnatinsa.
Al'amarin da ya zafafa rajin ballewa daga Najeriya a tsakanin
wasu matasan yanki a baya-bayan nan.
Sai dai, wani Igbo ya ce: "Za mu yi masa marhabin ta yadda zai
yi wa yankinsu wani aikin ci gaban kasa. Ai Najeriya kasarmu
ce."
Za mu yi murna da zuwansa, in ji shi.
Ita ma wata ta ce "Ai babu damuwa! Ina farin ciki da haka.
Ziyarar za ta sa mu ji cewa Najeriya daya ce babu batun nuna
bambanci tsakanin Bahaushe ko Bayarabe ko Igbo."
Ta ce wato dukkan al'ummar kasar daya suke. "Ina kaunar
wannan ziyara da Buhari da zai kawo yankinmu".
Haka zalika, mutanen yankin na Kudu Maso Gabas na zargin
gwamnatin Buhari da rashin gudanar da ayyukan raya kasa,
inda suka ce yana nuna fifiko a mulkinsa.
Shi kuma wani tsohon dan jarida a yankin, Kalu Ezee na cewa
da ma ya kamata Buhari ya kai wannan ziyara.
A cewarsa tun da aka kammala zabe, Buhari bai samu damar
ziyartar yankin ba, don haka zuwansa zai magance wasu
abubuwa da dama.
"Ka san mutanenmu kafin ya zo, suna gani kamar bai yi musu
wasu ayyukan alheri sosai ba, don haka wannan dama ce gare
shi ya fada musu abubuwan da ke zuciyarsa," in ji Mista Kalu.
Ya ce mutanen yankin su ma za su samu damar yi masa
bayani game da matsalolin da suke ci wa al'ummar yankin
tuwo a kwarya.
A cewarsa: "Za su yi masa magana a kan (mawuyacin hali da)
hanyoyin gwamnatin tarayya da ke yanki. Za su yi magana a
kan (aikin) gadar Neja ta biyu, wato gadar nan ta Onacha, ka
san ta dade ana maganarta."
Dan jaridar ya ce al'ummar yankin za su so su bijirowa da
Shugaba Buhari batun samar da ayyukan yi ga matasa da kuma
tsaro.
"Za su yi magana game da rikicin nan da ke faruwa tsakanin
manoma da makiyaya, Mista Kalu ya ce.
An tambaye shi ko za a bijiro wa shugaban maganar kafa kasar
Biafra sai ya ce: "Maganar Biafra ba za ta taso ba, don kuwa
kungiyar Ohaneze Ndigbo ta rika ta magance al'amarin".
Kadanna WANNAN Bulan rubutu don samun labarai
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment