Thursday, 9 November 2017

Nigeria: Wane bangare Buhari zai fi kashe wa kudi a kasafin 2018?


Najeriya ta bayyana kasafin kudinta na 2018, wanda
gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke fatan zai samar
da yanayin cigaba daga halin karayar tattalin arzikin da kasar
take fama da shi.
Shugaba Buhari ya bayyana kasafin kudi na Naira tiriliyan 8.6 a
gaban majalisar kasar, wanda ya ce zai samar da ayyukan yi ga
matasa da kuma sabbin gine-gine a kasar.
A bana ne Najeriya ta fita daga matsalolin koma-bayan tattalin
arziki a hukumance bayan faduwar farashin man fetur, a
shekarun baya.
A jawabin da ya gabatar, shugaba Buhari ya ce Najeriya: "ba za
ta yi sakacin komawa cikin rikice-rikicen da suka addabi kasar
a shekarun baya a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ba.
Kasafin na bana ya zarce na bara da karin kaso 16 cikin 100
kuma gwamnatin Najeriya ta ce za ta mai da hankali wajen
samar da hanyoyi da kiwon lafiya da gidaje da kuma samar da
ayyukan yi.
Jadawalin manyan ma'aikatun da suka samu kaso ma fi yawa
a wannnan kasafin kudin na 2018 ya nuna cewa ayyuka raya
kasa ne ke kan gaba.
A karkashin kasafin kudin na bana, ma'aikatar Wutar Lantarki,
Ayyuka da Gidaje ce ta sami kaso ma fi tsoka na Naira biliyan
555.88.
Shugaba Buhari ya bayyana dalilin ba wannan ma'aikata kaso
mai yawa: "Gwamnati na son samar da sabbin ayyuka da za su
kawo cigaban tattalin arziki da raya kasa."
Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ce ke ta biyu, inda aka ware
mata Naira biliyan 510.87, daga nan sai ma'aikatar Ilimi da
zata sami Naira biliyan 435.01.
Daga nan kuma sai ma'aikatar Tsaro da zata sami Naira biliyan
422.43, sai ma'aikatar Kiwon Lafiya da aka ware mata Naira
biliyan 269.34.
Ma'akatar Sufuri an ware mata Naira biliyan 263.10, inda aka
ba ma'aikatar Noma da Raya Karkara Naira biliyan 118.98.
Sai kuma ma'aikatar Albarkatun Ruwa da za ta sami Naira
biliyan 95.11, sai kuma ma'aikatar Ma'aikatu da Cinikayya da
Zuba Jari mai kason Naira biliyan 82.92
Amma ana sa ran gibin dake tsakanin kasafin kudin shiga da
ainihin wadanda za su shiga lalitar gwamnati zai ragu daga
Naira tiriliyan 2.36 na kasafin kudin bara zuwa 2.005 a kasafin
kudin bana.
Kasafin kudin dai zai zama doka ne kawai idan 'yan majalisar
kasar suka amince da shi.
Bangaren gwamnati da na majalisa sun sha kai ruwa rana kan
kasafin kudi musamman wanda ya gabata, al'amarin da har ya
kai ga tonon silili tsakanin 'yan majalisar.

No comments:

Post a Comment