Wednesday, 15 November 2017
Must read-An yi wa Shugaba Mugabe 'daurin talala' a Zimbabwe
Sojojin Zimbabwe sun yi wa Shugaba Robert Mugabe daurin
talala a babban birnin kasar Harare, in ji shugaban Afirka ta
Kudu Jacob Zuma.
Mista Mugabe ya shaida wa Mista Zuma ta wayar tarho cewa
yana cikin koshin lafiya, in ji ofishin shugaban Afirka ta Kudun.
Sojoji sun ta yin sintiri a babban birnin kasar, Harare, bayan
sun karbe iko da gidan talabijin din kasar kuma sun ce suna
hakon masu laifi ne.
Wannan yunkurin ka iya kasancewa kokarin maye gurbin Mista
Mugabe da mataimakinsa da aka kora, Emmerson
Mnangagwa, in ji wakiliyar BBC.
Korar Mista Mnangagwa a makon da ya wuce ya sa ana ganin
matar Mista Mugabe, Grace, ce za ta gaje shi a mulki.
Mista Mugabe, mai shekara 93, ya mamaye fagen siyasar kasar
tun da ta sami 'yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1980.
Bayan an shafe kwanaki ana zaman dar-dar da kuma yada jita-
jita, sojoji sun karbe iko da kafar watsa labarai mallakar
Zimbabwe, ZBC cikin daren ranar Talata.
Wani jami'in sojin Zimbabwean, Manjo Janar General Sibusiso
Moyo, ya yi wani jawabi a gidan talabijin mallakar kasar cewa
babu wani juyin mulki a kasar, amma ya ce sojojin suna hakon
masu laifi ne da ke kewaye da Shugaba Mugabe.
Jaridar Chronicle wadda ke karkashin ikon gwamnatin
Zimbabwe a birnin Bulawayo, ta wallafa labarai na musamman
game da rikicin kasar.
Ta fito da kanun da ke cewa: "Sojoji sun karbe iko", tana mai
cewa sojoji sun karbe mulki domin su "kakkabe masu laifuka
na jam'iyyar ZANU-PF".
Me ya sa sojoji ba sa son amfani da kalmar juyin mulki
Rashin ambatar kalmar juyin mulki shi ne abun da ya fito cikin
jawabin da manjo janar Sibusiso Moyo ya gabatar a kafar yada
labaran Zimbabwe ZBC, da safiyar Laraba.
Janar Moyo ya jaddada cewa wannan ba juyin mulki ba ne.
Saboda haka me ya sa wannan yake da muhimmanci?
Kungiyar Tarayyar Afirka AU, da kuma kungiyar raya kasashen
kudancin Afirka (Sadc), ba su lamunci juyin mulki ba.
An ga hakan ya faru a Burkina Faso a shekarar 2015 a lokacin
da kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Burkina Faso ta kuma
kakaba takunkumi kan wadanda suka yi yunkurin juyin mulki,
shekara daya bayan an tumbuke Blaise Compaore wanda ya
dade yana mulkar kasar.
Ba abun mamaki ba ne cewa rundunar sojin kasar tana ta
kokarin nuna cewa farar hula ce take iko da kasar har yanzu.
Tuni dai, Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya fitar da
wata sanarwa a madadin SADC cewa yankin ba zai lamunci
juyin mulki ba.
'Sojoji na dukan 'yan sanda'
Wata mata da ke zaune a Harare, Denissa Moyannah, ta
shaida wa BBC cewa ta kai ziyara tsakiyar birnin, daga gidanta
da ke unguwar masu hannu da shuni ta Borrowdale da safiyar
Laraba.
Ta ce motoci masu sulke sun cika ko ina a tsakiyar birnin inda
suke tsayar da ababen hawa a tsakiyar hanya.
Ta ce sojoji na dukan 'yan sanda, sannan kuma kafar talabijin
din kasar tana saka wakokin neman 'yanci.
Miss Moyannah ta kuma ce kura ta lafa a babban birnin
Zimbabwe din.
Domin zamun labarai kadanna WANNAN Bulan rubutu
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment