Saturday, 11 November 2017

An Kama Wani kafurin Boka Da Kasusuwan Mutane


WASHINGTON, DC — Rundunar ‘yan Sandan jihar Abia ta
damke wani Boka, bayan ta ta same shi da wasu bangarorin
mutane da kasusuwa.
Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Mr. Leye Oyebade, ne ya
shedawa manema labarai a garin Umuahia, cewa mutumin da
aka damke, ya kasa baiwa hukumomin wani dalili mai
gamsarwa a lokacin da akayi mashi tambayoyi.
Yana mai cewa kwarangwal din kai da wasu kasusuwan da
aka samu an zargin na irin mutanen da ake kashewa ne.
Wanda ake zargi ya musanta zargin yana mai cewa yayi
gadon sune a wurin wani kawun sa wanda shima boka ne
kafin rasuwarsa.
Yace mutanan su ne suka kai karansa wajen ‘yan Sanda
domin yana amfani da kasusuwan wajen yin siddabaru.
Ya kara da cewa duk wanda ya taba sai mazakutan say a
bace idan har kasusuwan na tare dashi.
Shi dai wannan Boka wanda kuma magini ne ya ce ‘yan
Sandan sun yi nasarar damke shine saboda asirin da yake
amfani dashi yayi balaguro, da cewa kama shi da akayi ba
daidai bane saboda haka ya bukaci da a sake shi.

No comments:

Post a Comment